30 Disamba 2021 - 15:24
​Masar: Girgizan Kasa Mai Ma’aunin Richter 5.9 Ta Awkawa Wasu Tsibirai A Kasar Girka

Hukuma mai kula da al-amuran girgizan kasa ta kasar Masar ta bada sanarwan cewa an yi girgisan kasa mai karfin ma’aunin Richter 5.9 a kusa da Tsibirin Crete wanda ya kai ga mutane a cikin kasar da dama a kasar sun ji kararta.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Jaridar Egypt today ta kara da cewa girgizan kasar mai ma’aunin Richter 5.4 ta awkawa tsibiran Cassos da Crete na kasar Girka ne a ranar litinin, sannan wata mai ma’aunin richter 5.2 ta sake aukawa tsibirin Crete, sa’o’i 4 bayan ta farkon, wanda ya kai ga wasu mazauna bakin Tekun Medeteranian a kasar Masar sun ji kararta.

Magajin garin tsibirin Cassos wanda yake kusa da inda abin ya auku ya bayyanawa kafafen yada labarai a birnin Athens babban birnin kasar Girkaka kan cewa girgizan kasar bata jawo wata asara ko ta ginegine ko ta rayuka ba.

342/